Makashin 'masu cin amanar ƙasa' ne ya kashe Jo Cox

Hakkin mallakar hoto Ross Parry
Image caption Mr Thomas Mair ya ki fadin sunansa na ainihi

Mutumin da ake zargi da kashe 'yan majalisar dokokin Biritaniya Jo Cox ya gurfana a gaban kotu ranar Asabar.

Da kotun Majistiret ta yankin Westminster ta buƙaci sanin sunan Mr Thomas Mair na ainihi, sai ya ce "Suna na makashin masu cin amanar ƙasa, wanda ke son 'yancin Biritaniya".

Mr Mair, mai shekara 52, ya ƙi fadin sunansa na gaskiya da kuma ranar da aka haife shi, har ma da adireshinsa.

Ana tuhumarsa da laifin kisan kai da mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba.

Yanzu dai ana ci gaba da tsare Mr Mair.

A ranar Alhamis ne aka harbe Mrs Cox , mai shekara 41, sannan aka daɓa mata wuƙa a Birstall da ke yankin West Yorkshire.

'Yar majalisar, wacce ke da aure da kuma 'ya'ya biyu, tana shirin kewaya mazaɓarta ne a lokacin da aka kai mata harin.