Ba a yi wa 'yan wasan Rasha adalci ba — Putin

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Putin ya bukaci hukumar da ke shirya gasar Olympic ta duniya ta sanya baki

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa ba a yi wa 'yan wasan motsa jiki na ƙasarsa adalci ba da aka hana su shiga wasannin motsa jiki ta duniya, ciki har da gasar Olympics da za a yi a Rio a shekarar 2016.

Hukumar kula da wasannin motsa jiki ta duniya dai ta ƙi janye haramcin da ta yi wa 'yan wasan Rasha na shiga gasar bayan an zarge su da yin amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari.

A cewar hukumar ɗai-ɗaikun 'yan wasan ƙasar za su iya shiga gasar idan suka bayar da shaidar da ke nuna cewa ba sa amfani da ƙwayoyin.

Mr Putin ya yi kira ga hukumar da ke shirya gasar Olympic ta duniya ta sanya baki cikin lamarin.

Hukumar ta ce za ta yi wani taro a kan batun ranar Asabar gabanin babban taron da za ta yi ranar Talata.