Turkey za ta farfado da Gezi park

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce zai sake waiwayar batun farfado da wurin shakatawa a tsakiyar birnin Santanbul.

Shi dai wurin shakatawar mai suna Gezi, na daya daga cikin dazuka da suka rage a birnin.

Mr Erdogan ya ce batun da ya shafi wurin shakatawar na Gezi abu ne da ya kamata yan kasar yin lale marhabun da shi, saboda manufar ita ce dawo da abubuwa masu dimbin tarihi.

Tsarin sake gina shin dai zai kunshi masallaci da kuma sake tada ginin tsohon barikin soji na zamanin daular Ottaman da kuma aza tubalin wasu muhimman gine-gine.

Tashin hankali

Mutane da dama ne dai aka hallaka tare da jikkata dubannai yayin wata zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati game da batun wurin shakatawar na Gezi a shekara ta 2013.

Tashin hankali ya kara ta'azzara bayan da yansandan kwantar da tarzoma suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

A sakamkon tashin hankalin na shekara ta 2013 ne wata babbar kotu a kasar ta Turkiyyar ta taka wa batun sake farfado da ginin birki, amma a bara ta janye matakin na ta bayan wata daukaka kara a birnin Santanbul.

Duk da haka wasu Turkawan na ganin sake gina tsohon barikin sojin na da matukar muhimmanci a tarihince.

Wasu shaidu sun ce shine barikin sojin da wasu sojoji masu kaifin ra'ayin addinin Islama suka yi tawayen da bai samu nasara ba a shekara ta 1909.

An kuma rushe barikin ne a shekara ta 1940, ta yadda wasu yan adawa ke kallon yunkurin sake tada gininsa a matsayin nuna amfani da addinin musulunci ne.