Jirgin ƙasa ya guntule ƙafar wani mutum

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata mata da ta sha giya ta taba fadowa daga jirgin kasa a Ingila

An gano ƙafa da yatsun wani da ake kyautata zaton jirgin ƙasa ne ya kaɗe shi a shekarar 2014 a ƙarƙashin wata tashar jirgi a Ingila.

Wani ɗan kwangilar da ke gyara tasoshin jiragen ƙasa ne ya gano sassan jikin mutumin a tashar jirgi ta Ingatestone a Essex ranar Alhamis.

'Yan sanda sun ce sun tuntuɓi iyalin mutumin kuma suna ci gaba da sanar da su halin da ake ciki.

An daina ɗauke sassan jikin daga wurin, kana aka shaida wa masu binciken gawarwaki.

Kakakin rundunar 'yan sandan Biritaniya ya ce ya yi amanna cewar ƙafa da yatsun na wani mutum ne da jirgi ya kaɗe a shekarar 2014, ko da ya ke gwaje-gwajen da za a yi wa sassan jikin ne za su gaskata ko ƙaryata iƙirarin nasa.