Ana bincike kan karkatar da abincin 'yan hijra

Image caption Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

Gwamnatin jihar Borno a Najeriya, ta fara bincike kan zargin da ake yi wa wasu jami'an hukumar agajin gaggawa ta jihar da karkatar da abincin da hukumar NEMA ke kai wa 'yan gudun hijra.

A wata sanarwa, gwamnan jihar Borno,Kashim Shettima ya umarci hukumar 'yan sanda tare da hukumar tsaro ta farin kaya da ke jihar da su gudanar da bincike sannan su kama duk wanda ake zargi da hannu a batun.

Wannan dai ya biyo bayan hoton bidiyon da aka saka a wasu shafukan sada zumunta da ya nuna wasu da ake kyautata zaton jami'an hukumar agajin gaggawa ta Jihar Borno ne, su na faman zuba shinkafar da hukumar NEMA ta kawo, a cikin wasu buhuna daban.

Malam Isa Gusau shi ne kakakin gwamnan jihar Borno, a hirarsa da Usman Minjibir, ya fadi cewa duk wanda aka kama da hannu a batun ba zai tsira ba, to sai dai kuma ya fara da bayyana shakkunsa kan al'amarin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti