Wata mata ta ceto danta daga bakin zaki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kiyasta cewa zakuna 4,500 na rayuwa a yankin Colarado

Wata mata a Colorado na kasar Amurka ta ceto danta mai shekara biyar daga bakin wani zaki, bayan da zakin ya cafki yaron a gaban gidansu.

Wani jami'in 'yan sanda na gundumar ya ce matar ta jiyo ihu ne sai ta bazama waje da gudu a gidan nasu da ke kusa da Aspen, inda ta ga zakin ya haye kan danta.

Yaron dai ya samu raunuka a fuska da kansa da wuya, an kuma garzaya da shi asibiti inda yake samun kulawa a Denver.

Daga bisani jami'ai sun kashe zakuna biyu.

'Da kyar na sha'

Matar wadda ba a fadi sunanta ba ta ce a kokarin ceton dan nata sai da ta damke kafar zakin guda daya ta sa hannunta da karfi ta bambareta daga jikin yaron ta kuma sa karfi ta bude bakin zakin ta fizgo kan danta da tuni yasa a bakin nasa.

Jami'in 'yan sandan Michael Buglione, ya ce ''Ita ma uwar duk zakin ya kakkarje mata fuska da hannu da kuma kafa, kafin ta samu fatattakar zakin mai kimanin shekara biyu.''

Al'amarin ya faru ne ranar Juma'a da daddare a kudancin Aspen.

Jami'ai sun ce ana yawan ganin zakuna a yankin Colarado, inda aka kiyasta cewa zakuna 4,500 na rayuwa a wajen.