'Toshe kafofin sada zumunta a Ghana bai dace ba'

Image caption Mohammed Ibn Chambas tare da soja a jamhuriyar Niger

Wakilin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, a kasashen Afirka ta Yamma da yankin Sahara, Dokta Muhammed Ibn Chambas ya ce, majalisar ta yi tir da duk wani shiri na toshe kafofin sada zumunta a Ghana.

Muhammed Ibn Chambas ya ce, matakin takaita amfani da kafofin sada zumunta zai kawo koma baya ga dimokradiyya a kasar ta Ghana.

A watan Mayu ne dai aka ambato supeto janar na 'yan sandan Ghana yana cewa, suna duba yiwuwar toshe kafofin sada zumunta a duk fadin Ghana, a ranar zaben shugaban kasar, wato 7 ga watan Nuwamba.

Wannan batu dai yana cigaba da janyo kace-nace a Ghana.