DSS sun yi tufka da warwara — Shi'a

Image caption Mabiyan Elzakzaky suna neman a sake shi.

Kungiyar 'yan uwa musulmi ta Islamic Movement in Nigeria ta mabiya mazhabin Shi'a ta ce hukumar jami'an farin kaya ta DSS ta yi baki biyu kan tsare shugabansu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky.

A farkon makon nan ne dai hukumar ta DSS ta yi ikirarin cewa tana cigaba da tsare Elzakzaky ne bisa radin kansa da kuma kare shi daga wadanda za su cutar da shi.

Hakan ya biyo bayan karar da lauyan El-zakzaky ya shigar a kotu na neman a sake shi.

Watanni shida ke nan dai ana tsare da Ibrahim El-zakzaky, tun bayan da sojoji suka yi wa 'yan kungiyar dirar mikiya bisa zargin yunkurin kashe shugaban sojojin kasar, Yusuf Tukur Burutai, zargin da mabiya shi'ar suka sha musantawa.

'An binne 'yan Shi'a 347 a kabari daya a Nigeria'

' Yan Shia sun kaurace wa kwamitin bincike

Yanzu haka dai 'yan kungiyar ta IMN sun yi Allah-wadai da ci gaba da tsare shugaban nasu.

A wata sanarwa da ta fitar a Kaduna, kungiyar ta ce ba ta amince da ikirarin da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kasar ta yi ba, na cewa tana tsare da El-zazzaky ne don tsaron lafiyarsa, da kuma don radin kansa.

Ibrahim Musa, shi ne shugaban majalisar 'yan jarida ta kungiyar Islamic Movement, ya kuma shaida wa wakilinmu na Kaduna, Nurah Mohd Ringim, cikakken matsayin kungiyar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti