Za a rufe kantunan giya 500 a India

Image caption Mata a Indiya na fuskantar cin zarafi daga mashaya giya

Jihar Tamil Nadu da ke kudu maso gabashin Indiya za ta rufe kantunan sayar da barasa 500, a wani mataki da dakatar da rikici.

Za kuma a rage tsawon sa'o'in da ake bude sauran kantunan da ake sayar da barasar.

Sabon gwamnan da aka zaba ne ya yi alkawarin daukar wannan mataki a lokacin da yake kamfe dinsa a watan da ya gabata.

Masu aiko da rahotannin sun ce an yi hakan ne domin kare mata wadanda su ne suka fi fadawa sharrin da giya ke haifarwa inda suke fuskantar cin zarafi da barazanar fyade daga mashaya.

Tuni dai yawancin jihohin Indiya suka haramta sayar da barasa.