Nigeria: Bita-da-kulli ake yi mana — Majalisa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption An dade ana samun rashin jituwa tsakanin gwamnati da shugabannin majalisar

Majalisar dattawan Nigeria ta zargi bangaren zartarwa da yunkurin kawo cikas ga dimukradiyya ta hanyar yin bita-da-kulli ga shugabannin majalisar.

Majalisar ta kuma ja hankalin kasashen duniya ga abin da ta kira wani yunƙurin banganren zartarwa da zai jefa dimokradiyyar Nigeria cikin hatsari.

A ta bakin kakakinta, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, majalisar ta yi wannan korafi ne saboda rahotanni dake cewa gwamnati na shirin gurfanar da shugabanninsu a gaban kotu.

Ya ce ana shirin gurfarnar da Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekeweremadu a gaban kotu, bisa zargin yin zagon kasa tare da yin jabun dokokin majalisar, a lokacin da aka zabe su.

Sanarwar wadda majalisar dattawan Najeriya ta wallafa a shafukanta na Facebook da Twitter ta ce, matakin wani shiri ne na gwamnatin tarayya na murkushe bangaren majalisar.

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Sanata Ekweremadu da Saraki sun musanta zargin da ake yi musu

Sanarwar ta kuma ce, gwamnatin tarayya tana daukar matakan ne da nufin sauya shugabannin majalisar dattawan.

Majalisar dattawan ta kuma yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya ja kunnen ministan shari'a, Abubakar Malami,da ya daina yi musu katsalanda.

Da ma dai shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki yana fuskantar wata shari'ar daban, kuma bisa ga dukkan alamu wannan batu zai bude wani sabon babi na sa-in-sa tsakanin majalisar dattawan da bangaren zartarwa.