'Yan bingida suna kai hari a Ogun

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website

Wasu 'yan bindiga da sun kai hari a yankin Kereko-Ogijo na jihar Ogun inda hukumomi suka ce an kashe mutane uku.

Kwamishinan 'yan sanda na jahar Abdulmajid Ali ya fadawa BBC cewa, mutane uku aka kashe, kuma wasu mutanen biyu sun …ďata.

Sai dai mazauna yankin da lamarin ya auku sun ce, mutane 15 aka kashe yayin harin.

Wata majiya ta ce, 'yan bindigar sun kai harin ne saboda suna zargin jama'ar yankin da taimakawa 'yan sanda da bayanai akan ayyukansu.

Rahotanni na cewa, 'yan bindigar sun aukawa yankin dauke da manyan bindigogi, da kuma wasu makamai ranar Asabar.