'A ba mu kariya da fansho na har abada'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Idan aka amince da kudurin Saraki da Dogara ne za su fara morarsa

'Yan majalisar dokokin Najeriya sun bukaci a bai wa shugabanninsu rigar kariya da fansho na har abada, har bayan sun sauka daga mukamansu.

Sun gabatar da wannan bukata ce a wani taron kwana biyu na sake duba kundin tsarin mulkin kasar da aka yi a birnin Lagos.

A cewar 'yan majalisar, jami'an da za su mori fansho na har abada su ne shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa da kuma shugaban majalisar wakilai da mataimakinsa.

'Yan majalisar sun kuma ce shugabannin majalisar sun cancani samun wannan moriya ta kariya, tunda 'yan bangaren zartarwa da na shari'a ma suna mora.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu ne ya fara gabatar da wannan bukata a wajen taron.

'Yan majalisa 21 sun goyi bayansa yayin da 15 kuma suka ki goyon bayan kudurin.

Idan har wannan kuduri nasu ya kai gaci aka sanya shi a kundin tsarin mulkin kasar, to za a janye tuhumar da ake wa Sanata Bukola Saraki a kotun da'ar ma'aikata.