Al-Shabab ta kona 'yan sandan Kenya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Al Shabab da ke Somaliya na yawan kai hari Kenya

Mayakan kungiyar al-Shabab ta Somalia sun kashe wasu jami'an 'yan sandan Kenya guda biyar bayan da suka yi musu kwanton bauna a Arewa maso Gabashin kasar.

'Yan sandan na yi wa wasu fasinjoji rakiya ne a wata motar bas zuwa garin Mandera.

Cibiyar Al Shabab dai na kasar Somalia ne da ke makwabta da Kenya, amma sun sha kai hari garin Mandera da kewaye.

Babban jami'in 'yan sanda na Mandera Job Boronjo, ya ce mayakan sun kona 'yan sanda ta yadda ba za a gane gawarsu ba, bayan kisan nasu.

Mista Boronjo ya kuma shaida BBC cewa, baya ga 'yan sanda da aka kashe, an kuma ji wa wasu hudu rauni.

A shekarar 2014 kungiyar Al Shabab ta kashe fiye da mutane 60 a wasu hare-hare guda biyu kusa da garin Mandera.