Jagoran Shi'a na Bahrain na tsaka-mai-wuya

Image caption Sheikh Isa Qassim shi ne jagoran mabiya shi'a a Bahrain

Bahrain ta soke takardun shaidar zama dan kasa na Isa Qassim, jagoran mabiya akidar Shi'a na kasar.

Wata sanarwar ma'aikatar cikin gida ta kasar ta zargi Sheikh Qassim da yin amfani da matsayinsa wajen "biya wa 'yan kasashen waje bukatu" da yada "kiyayya ta addini da kuma tashin hankali".

Malamin Shi'ar wanda ya ke da matsayin Ayatollah, ya goyi bayan zanga-zangar mafi yawan al'ummar 'yan Shia a kan 'yancin kai da kuma na siyasa.

Rahotanni sun ce Sheikh Qassim, wanda aka haifa a Bahrain, ba shi da wata takardar shaida banda ta kasar ba.

A makon da ya gabata ne gwamnati ta dakatar da babbar jam'iyyar adawa ta 'yan shia.

Hukumomi a Bahrain sun ce an rufe ofisoshin kungiyar al'ummar Musulmai na kasa Wefaq, kuma an hana su taba kadarorinsu.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi Allah-wadai da matakin da hukumomin suka dauka.

Mutanen da aka kwace wa takardun zama 'yan kasa na da ikon daukaka kara amma a lokuta da yawa ba sa samun nasara.