Na ji dadin dawowa aiki - Buhari

Buhari da Osinbajo Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption A safiyar ranar Litinin ne shugaba Buhari ya koma aiki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya ji daddin dawowa aiki bayan ya shafe mako biyu a London domin jinya da kuma hutu.

Mista Buhari ya wallafa hotonsa ya na zaune a ofis tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo a shafinsa na Twitter.

A ranar Lahadi da yamma ne shugaban ya koma Najeriya bayan ya je London domin jinyar ciwon kunnen da yake fama da shi bisa shawarar likitocinsa na cikin gida.

Bayan ya iso filin jiragen sama da ke Abuja, ya ce "ina jin karfin jikina" kuma ya kara da cewa " zan iya dambatawa da duk wanda ya ke so ya kara da ni".

'Yan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayoyinsu ga sakon na Mista Buhari, inda akasarinsu ke yi masa barka dawowa.

Chima John Paul, ya ce "muna yi maka barka da dawowa Sir, kamar yadda kake gani akwai abubuwa da ake bukatar yi. #fast [a hanzarta]".