Hanyoyi 5 da sabon tsarin dala zai shafe ku

Hakkin mallakar hoto Getty

A ranar Litinin ne matakin da babban bankin Najeriya (CBN), ya dauka na kyale kudin kasar ya samarwa kansa daraja a kasuwa domin shawo kan matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, ke fara aiki.

Mun yi nazari kan wasu hanyoyi biyar da wannan mataki zai iya shafar rayuwarku.

'Hauhawar farashi za ta karu amma...'

Masana sun yi ittifakin cewa farashin naira zai kara faduwa da zarar wannan tsari ya fara aiki, abin da zai kara haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

Tuni dai 'yan kasar suka dade suna ji a jikinsu sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya da kuma matakin gwamnati na kare darajar naira.

Sai dai masanan sun ce darajar naira za ta farfado kuma farashi zai fara sauka idan tafiya ta yi tafiya.

Abin tambaya anan shi ne ko mutane za su iya jurewa wani karin hauhawar farashi banda wanda suke ciki a yanzu?

Wasu dai na ganin tura ta kai bango.

'Farashin man fetur ba zai tashi ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Farashin man fetur ba zai karu ba

A cewar masanin tattalin arziki Feyi Fawehinmi, tataccen man fetur, wanda shi ne abin da aka fi shigowa da shi kasar, zai tsaya a kan sabon farashinsa na naira 140 zuwa 145.

Kuma ana sa ran babban bankin zai fara wannan sabon tsari ne ta hanyar musayar naira 285 a kan dala $1, domin tabbatar da cewa farashin man bai tashi ba.

Wannan wani labari ne mai dadin ji ga jama'a domin yana nufin cewa harkokin sufuri da sauran abubuwan da suka dogara a kan man fetur za su cigaba da kasancewa yadda suke.

A don haka, za a iya cewa jama'a sun yi bankwana ga dogayen layukan mai idan har fatan da ake da shi ya dore.

'Masu shigo da kaya na tsaka mai wuya'

Image caption Akwai yiwuwar shinkafa da sauran kayan masarufi su kara tashi

Wannan tsari da ya fara aiki bai sauya wasu muhimman matakai da CBN ya dauka ba na hana bayar da dala domin shigo da wasu kayayyaki 41 zuwa kasar ba.

Kayan sun kama daga tsinken sakace zuwa jiragen sama masu zaman kansu.

Sai dai babban abin da ya fi damun mutane shi ne illar hakan kan farashin shinkafa - wacce ita ce abincin da aka fi ci a kasar.

Farashinta ya yi tashin gwauron zabi, kuma babu alamar cewa wannan sabon tsarin zai yi tasiri kan farashinta da ma na sauran wadannan kayayyaki, abin da zai kara jefa jama'a cikin mawuyacin hali.

Sai dai wannan mataki labari ne mai dadin ji ga masu sarrafawa da sayar da man abinci wadanda suka samu karin kasuwa sakamakon matakin na CBN.

'Ma'aikatan bankuna na cikin hadari'

Image caption CBN ya ce bankunan kasar sun gaza biyan basukan da ake bin su

CBN ya ce a kalla kashi 10 cikin 100 na bashin da ake bin a bankuna kasar ya gagara biya.

Yawancinsu basuka ne na kudaden waje da aka baiwa masu hada-hadar man fetur da iskar gas a lokacin da danyan mai ke da daraja.

Faduwar darajar naira ya jefa bankunan cikin tsaka mai wuya, abin da wasu suka alakanta wa da korar ma'aikatan da wasunsu suka rinka yi a 'yan kwanakin da suka wuce.

Cigaba da gazawa wurin biyan basukan na nufin kara korar wasu ma'aiktan.

Abin jira a gani shi ne yadda gwamnati za ta bullowa lamarin tun da ganin yadda ta nuna adawa da korar ma'aikatan a baya.

'Masu zuba jari za su shigo'

Image caption Ayyukan yi za su samu idan masu zuba jari suka shigo

Wani labari mai dadin ji shi ne ganin yadda masana ke cewa wannan sabon tsarin na CBN zai karfafa gwiwar masu zuba jari na kasashen waje da suka dade suna dari-dari game da zuba dukiyarsu a kasar.

Hakan zai iya bunkasa tattalin arzikin kasar da samar da ayyukan yi.

Suma kamfanonin jiragen sama na kasashen waje za su samu nutsuwa, domin kudaden da suke bi bashi za su fito. CBN ya ce ana binsa jumullar kudaden da suka kai $4bn.

Wannan zai sa kamfanonin jiragen, wadanda wasunsu suka janye daga kasar, su ci gaba da zuwa.

Hakan zai kara farfado da martabar kasar a idanun duniya.