Iran ta dakile yunkurin harin mayakan Sunni

Ma'aikatar lekan asirin Iran ta ce hukumomi a kasar sun dakile yunkurin harin mayakan 'yan Sunni a Tehran babban birnin kasar, da ma wasu biranen.

Ma'aikatar ta ce an kama wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar 'yan ta'addar ta "Takfiri" kuma an kwace wasu nakiyoyi daga hannunsu.

Sai dai ma'aikatar lekan asirin Iran din ba ta yi karin bayani a kan wadanda ake zargi ba.

"Takfiri" dai wata kalma ce da 'yan Shia 'yan kasar Iran ke amfani da ita domin bayyana 'yan Sunni masu tsattsaurar ra'ayi wadanda ke yi wa wasu Musulman kallon marasa addini.

Iran na da hannu dumu-dumu a rikicin da ake yi da kungiyar IS a kasashen Iraki da Syria.

Tana kuma marawa 'yan tawayen Houthi masu bin akidar Shi'a baya a kasar Yemen.

Masu tayar da kayar baya da ke ikirarin kare hakin al'ummar Sunni da ba su da rinjaye a Kudu maso Gabashin kasar sun sha kaiwa gwamnati hare-hare a baya-bayan nan.Iran police