Manajan kamfe na Trump zai bar aikinsa

Hakkin mallakar hoto Getty

Manajan yakin neman zaben dan takarar shugabancin Amurkar Donald Trump, zai bar aikinsa.

Wata mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben Mita Trump din ta ce, tawagar yakin neman zaben dan takarar ta jinjina wa Lewandowski saboda aiki tukuru da kuma sadaukarwa.

Ba a san takamaimai dalilin da yasa Mista Lewandowski zai bar aikinsa ba tukuna.

Tafiyarsa na zuwa ne yayin da Mista Trump ke fuskantar turjiya mai karfi daga manyan mambobin jam'iyyarsa saboda wasu kalamansa marasa dadi da kuma manufofinsa masu tsauri a kan 'yan cirani.

Cikin masu sukarsa akwai kakakin majalisar wakilai da kuma wani mai rike da babban mukami a jam'iyyar Republican Paul Ryan, wanda ga alamu ya bar kofar da za a iya juyawa Donald Trump din baya a bude, a lokacin babban taron da jam'iyyar za ta yi a watan gobe.

Da aka tambayeshi ranar Lahadi game da rahotannin da ke cewa wakilai a jam'iyyarsa ka iya yiwa Mista Trump tawaye a babban taron jam'iyyar sai ya ce: '' Muna rubuta dokokin, muna kuma yanke shawarar.''

An caccaki Mista Trump saboda irin martanin da ya mayar bayan kisan mutane 49 a garin Orlando na Amurka.