Taliban ta sace mutane 25

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Taliban ta sace mutane 25

Rahotanni daga Afghanistan sun ce mayakan kungiyar Taliban ta sace wasu mutane 25 da ke tafiya a wasu manyan motoci.

Mayakan sun tsayar da motocin ne inda suka umarci mutanen da su fito, sannan suka yi awangaba da su.

Yan sanda a lardin Helman, inda aka yi samamen, sun ce motar safa-safa din na dauke da kusan mutane dari.

Sai dai jami'ai sun ce an saki wasu daga cikin mutanen wadanda suka hada da mata 18 da kuma yara.

Wani mai magana da yawun kungiyar Taliban Qari Yasuf Ahmadi ya tabbatar cewar su su ka yi samamen inda ya kara da cewa wani bangare ne na abinda ya kira aikin bincike.

A 'yan watannin baya-bayan nan kungiyar ta fara sace jama'a abinda a baya ba a santa da aikatawa ba.