An tafka muhawara kan ficewar Biritaniya daga EU

Hakkin mallakar hoto Getty

Manyan kusoshin da ke kamfe na ficewa ko kuma cigaba da kasancewar Birtaniya a kungiyar tarayyar Turai, EU sun tafka zazzafar muhawara.

Sun yi muhawara mafi girma da aka taba yi kai-tsaye a gidan talabijin, gabanin zaben raba-gardamar da za a yi ranar Alhamis.

Tasirin da batun zai yi a kan tattalin arziki da kuma batun harkokin shige-da-fice su ne manyan tambayoyin da suka rika fitowa daga bakunan mahalarta taron dubu shida.

Tsohon magajin garin birnin London Boris Johnson - wanda ke son a fice din - ya ce ayyukan gwamnati na fuskantar matsin lamba saboda abind a ya kira batun harkokin shige-da-fice na kungiyar Tarayyar Turai.

Sai dai mutumin da ya gaje shi, Sadiq Khasn, ya ce tattalin arzikin kasar zai fada mawuyacin hali idan ta fice daga tarayyar Turai.

Wasu kuri'un jin ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare game da sakamakon.