An nada sabon Sufeton 'yan sandan Nigeria

Image caption Kpotum zai maye gurbin Mista Solomon ne a matsayin shugaban 'yan sandan kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Kpotum Idris, a matsayin sabon Sufeton rundunar 'yan sandan kasar.

An nada shi ne bayan saukar Solomon Arase, wanda ya kammala aiki bayan ya cika shekara 60 a duniya.

Kpotum zai maye gurbin Mista Solomon ne a matsayin shugaban 'yan sandan kasar.

Kafin sabon matsayinsa, Mista Kpotum ya rike matsayin mataimakin sufeton 'yan sandan mai kula da ayyuka na a hedikwatar 'yan sandan da ke Abuja.

Kpotum Idris dai mutumin jihar Naija ne da ke arewacin kasar.