Masar ta yi amai ta lashe

Image caption A watan Afrilu ne shugaban Masar ya sanar da mayar da tsibiran ga Saudiya

Wani alkali a Masar ya yi watsi da matakin ga gwamnatin kasar na bayar da wasu tsibirai guda biyu na tekun Bahar-rum ga kasar Saudiyya.

A watan Afrilu ne Shugaban Masar, Abdul Fattah al--Sisi ya sanar da mayar da tsibiran Tiran da Sanafir a lokacin da Sarki Salman na Saudiyan ya kai ziyara kasar.

An tsare mutane sama da 150 a gidan kaso a kan wata zanga-zanga da suka yi a kan yarjejeniyar, ko da ya ke dai daga bisani ba a kama wasu da laifi ba sannan an bukaci a rage yawan hukuncin da a ka yankewa wasu.

Hukunci dai wanda aka yanke a ranar Talata, ba shi ne hukunci na karshe ba kuma babbar kotu za ta iya sauya shi.

Sai dai kuma babu mutanen da su ke rayuwa a kan tsibiran na Tiran da Sanafir da ke Aqaba da ke Arewacin Bahar-rum.

Matakin na shugaba Sisi ya haifar da tarzoma a sassan kasar daban-daban.

Shugaban ya kare matakin yana mai cewa dama asalin tsibiran mallakar kasar ta Saudiyya ne.