Facebook ya cire kafar bidiyo daga wasu shafukan internet

Hakkin mallakar hoto Getty

Facebook ya janye kafar da masu kirkirar faya-fayen bidiyo ke bi su makala hanyoyinsu ta cikin shafinsa.

Wannan kafa dai na da tagomashi wajen kafafen yada labarai da kan yi amfani da ita wajen jan hankulan mutane su rika duba shafukansu.

An dai sauya wannan tsari ne a farkon wannna wata ba tare da wata sanarwa ba.

Kwararru sun ce matakin wata alama ce da ke nuna yadda Facebook din ke da karfin ikon sanin yadda jama'a ke karantawa da kuma kallon labarai a shafinsa.

Kamar yadda wani bincike na baya-bayan nan ya nuna, kashi 28 bisa dari na mutanen Birtaniya na amfani da Facebook a matsayin hanyar samun labarai akalla sau daya a mako daya, yayinda adadin ke karuwa zuwa kashi 41 bisa dari na 'yan kasa da shekaru 35.