An kashe Jo Cox ne saboda siyasa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A makon da ya gabata ne aka kashe Jo Cox

Mai gidan Jo Cox, 'yar majalisar dokokin Birtaniyar nan da aka kashe ya ce ya yi amannar an kashe matarsa ne saboda irin ra'ayoyinta na siyasa.

A hirarsa ta farko bayan kashe ta, Brendan Cox, ya ce ko bayan mutuwarta, idan da hali za ta tsaya tsayin daka kan ra'ayoyinta na siyasa kamar yadda ta yi a lokacin da ta ke a raye.

Sai dai ya ce tana girmama cewar mutane za su iya kin yarda bisa ra'ayoyinta.

Amma ya kara da cewa matarsa ta damu da inda kuri'ar raba gardamar Birtaniya a Tarayyar Turai ta dosa, inda ta ce lamarin na jawo tsoro da kiyayya.

An dai harbe sannan aka sokawa 'yar majalisar wuka, inda aka kashe ta har lahira a makon da ya gabata a lokacin da ta ke shirin ganawa da mazabarta da ke arewacin Ingila.

Ita dai Cox na cikin 'yan siyasar Birtaniya da ke son Birtaniya ta ci gaba da zama a Tarayyar Turan.