Jordan ta rufe iyakarta ta Iraqi ta Syria

Hakkin mallakar hoto

Kasar Jordan ta ayyana rufe kan iyakarta da kasashen Syria da Iraqi, sakamakon mummunan harin bam din da ya hallaka sojoji shida ranar Talata.

An kaddamar da harin ne daga gefen kasar Syria kusa da sansanin 'yan gudun hijira.

Gwamnatin kasar Jordan ta ce ba za a sake gina sabbin sansanonin 'yan gudun hijrar ba, kana ba za a fadada ko daya ba.

Gwamman mutane ne ke gudanar da taron addu'oin tare da kunna kyandira a Amman babban birnin kasar don tunawa da wadanda harin ya rutsa da su.

Babu dai tabbaci kan ko su wanene ke da alhakin kaddamar da harin.