Majalisar Amurka ta daure wa 'yan bingida gindi

Shugaba Barack Obama Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Obama ya ce matsalar na tattare da rashin sanya takunkumi kan yadda ake sayar da bindiga

Majalisar dattawan Amurka ta yi watsi da kudirin dokar da ke son a sanya ido sosai kan yadda ake sayar da bindigogi, ciki har da sayar wa 'yan ta'adda makamai.

An dai gabatar wa majalisar kudurorin doka hudu domin ta yi musu gyaran fuska, bayan harin da Omar Mateen ya kai gidan dabdalar 'yan luwadi a Florida, inda ya harbe mutum 49.

Sanatocin sun nuna rashin amincewar su kan matakin da za a dauka domin hana kai hare-hare a kasar.

Dan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican John Cornyn ya ce batun kawar da ta'addanci shi ne ya kamata majalisar ta mayar da hankali akai.

"Abokan aiki na suna batu kan yadda za a sa ido kan yadda ake sayar da bindigogi, amma a gani na ya kamata mu mayar da hankali kan yadda za a kawar da ta'addancin masu kishin Islama, domin hakan ne ya kawo harin da aka kai Orlando."

Ita kuwa 'yar majalisa daga bangaren Democrat Barbara Mikulski katanta lamarin ta yi da yadda ake bincike a filayen saukar jiragen sama.

Ta ce: "Me ya sa muke mayar da hankali kan yadda ake caje mutane a lokutan da za su hau jirgin sama domin hana aukuwar ta'addanci, amma ba ma mayar da hankali kan mutanen da ke jerin wadanda ka iya kai hare-haren ta'addanci?"

'Yan jam'iyyar Republican da kuma 'yan kungiyar masu sayar da bindigogi dai sun ce hana sayar da bindigogin tamkar take hakkin mutane ne.