Ce-ce-ku-ce kan dokar hukunta mazinata a Kamaru

Image caption Shugaba Paul Biya na Kamaru ya ce an yi kudurin ne don a samar da daidaito tsakanin jinsuna

Majalisar dokokin jamhuriyar Kamaru ta fara mahawara a kan wani kudurin doka da ke neman hukunta masu aure a kasar da aka kama da yin zina.

Wannna kudirin dai ya tayar da ce-ce ku ce a kasar, kuma bai samu cikakken goyon baya ba musamman ga kungiyoyin kare hakkin Bil adama.

Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar ma ba sa goyon bayansa.

Sai dai gwamnati ta ce ta kuduri aiwatar da dokar ne domin yin adalci tsakanin jinsuna.

Sharhi, Muhamman Babalala, sashen Hausa na BBC, daga Kamaru

Hakkin mallakar hoto babalala
Image caption Muhamman Babalala shi ne wakilin BBC a jamhuriyyar Kamaru

Wannan kudurin doka da gwamnati ta mikawa 'yan majalisa don ta nazarta ya kunshi wasu fannonin da suka shafi rayuwar bil'adama, kamar ladabtar da duk wani mai auren da aka kama da yin zina da kuma mabarata.

An bullo da wannan dokar ne domin bukatar samar da daidaito a tsakanin mata da maza. A waccar tsohuwar dokar a kan hukunta mata masu auren da aka kama da yin zina ne kawai ba tare da hukunta mazan ba.

To amma da yake wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama na nuna adawa da dokar, sai gwamnati take kokarin gamsar da su cewa tana son samar da daidaito ne tsakanin jinsuna, ba wai kawai a dinga ladabtar da bangare daya ana barin daya ba.

Mata dai sune wadanda suka fi nuna farin ciki da gamsuwarsu kan wannan kudurin doka, tunda suna ganin an samu hanya ta ladabtar da mazajen da ke cin amanar aure.

Matan suna ganin duk da cewa a baya dokar su kadai ta shafa amma da wuya a samu matar aure da aikata irin wannan laifi balle har ta yi zaman gidan yari, a ganinsu maza ne suka fi yin laifin kuma dokar bata hawa kansu.

'Matsayar kafofin yada labarai kan kudurin'

Wannan kudurin doka dai bai samu karbuwa ba ta bangare da dama. Wasu na ganin hakan wani koma baya ne gwamnati ke son kawowa a irin wannan zamani na cigaba.

Sai dai gwamnati ta ce kafin ta yi wannan kuduri sai da ta tuntubi kowanne bangare na al'umma har zuwa kan sarakunan gargajiya, kuma shi ne dalilin da yasa ta mika wa 'yan majalisa kudurin.

Amma duk da sukar da gwamnatin ke sha kan kudurin, ta ce ba gudu ba ja da baya.