Bama bamai sun kashe mutum 25 a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai matasa da ke shiga sojin sa-kai a Libya da dama.

Akalla mutum 25 ne suka rasa ransu sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon wani tashin bam mai girman gaske, a Tripoli, babban birnin kasar.

Fashewar bam din dai, wadda ta faru a garin Garabulli, ta biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin mutanen garin da mayakan sa-kai daga birnin Misrata.

Da farko dai, wasu jami'ai a kasar sun fadawa BBC cewa al'amarin ya faru ne a wani wurin ajiyar makamai.

Sai dai wani mazaunin garin na Garulli ya shaida wa BBC cewa wata babbar mota ce cike da abubuwan fashewa ta tarwatse.