Shin ko kana amfani da Instagram?

Hakkin mallakar hoto INSTAGRAM
Image caption Yawancin mutane suna daukar hoton kansu mai suna 'Selfie' su tura cikin kafar ta Instagram.

Idan kana amfani da kafar sada zumunta ta Instagram, to kana cikin mutane miliyan 500 din da kamfanin ya ce suna mu'amila da shi.

Fiye da mutane miliyan 300 ne suke shiga kafar akalla sau daya, a kullum, in ji kamfanin.

A shekarar 2012 ne dai shafin sada zumunta na Facebook, ya sayi Instagram din a kan kudi dala biliyan daya, kwatankwacin Fam miliyan 677.

Kuma tun lokacin masu amfani da shafin na Instagram suke karuwa a kowace rana.

Kamafanin ya ce, a kullum ana dora akalla hotuna masu motsi da marasa motsi a kan shafin da suka kai yawan miliyan 95.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Instagram ya samu karbuwa a wurin jarumai

Daya daga cikin mutanen da suka kafa Instagram din, Kevin Systrom, ya shaidawa BBC cewa sun samu nasara ne sakamakon irin jajircewar da suka yi.

A shekaru biyar din Instagram na kafuwa, kafar ta wuce Twitter, saboda jarumai fina-finai da zakarun 'yan kwallo sun karbe ta hannu bibiyu.

Kafar sada zumunta ta Snapchat wanda ke gasa da Instagram, da kadan ta haura miliyan 100 na mutanen da ke amfani da ita.