Korea ta Arewa ta yi gwajin makamai masu linzami

Hakkin mallakar hoto XINHUA
Image caption Shugaban kasar Korea ta Kudu Park Geun-hye ya bayyana gwajin a matsayin wani yunkurin "na takalar fada."

Korea ta Arewa ta yi gwajin makamai masu linzami guda biyu dab da dab da juna, a wani mataki na bijirewa hanin da majalisar dinkin duniya ta yi na yin hakan.

Jami'an Korea ta Kudu sun ce makamin na farko ya ki tashi, yayin da na biyun kuma ya yi tafiyar nisan kilomita 400 a sararin samaniyar kasar, kuma daga bisani ya fada cikin teku.

Gwamnatin Japan ta yi tur da gwajin makaman, inda ministan tsaron kasar, Gen Nakatani, ya ce hakan na matukar barazana ga kasarsa.

Sau hudu makaman da Korea ta Arewa ta yi gwajin su a baya suka ki yin aiki.