Hillary babbar makaryaciya ce — Trump

Image caption Hillary da Trump na cigaba da jifan juna da kalaman batanci

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya yi kakkausar suka kan abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar Democrat Hillary Clinton, yana mai cewa ba ta da yanayi da kuma nutsuwar zama shugabar kasa.

A wani jawabi da ya gabatar a birnin New York, Mista Trump ya soki Misis Clinton da cewa ''babbar makaryaci ce ta inna naha,'' wadda ta azurta kanta a lokacin da take rike da mukamin sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Zuwa yanzu dai Misis Clinton bata mayar da martani kan wannan kalamai na Trump ba.

Sai dai a ranar Talata ne Misis Clinton ta soki Mista Trump inda ta ce, zabar hamshakin dan kasuwa mai harkar gidaje a matsayin shugaban kasar Amurka, zai zama wani babban bala'i ga tattalin arzikin kasar.

Masu aiko da rahotanni na cewa manyan abokan hamayyar suna kara zafafa sukar juna da kalaman batanci a kokarinsu na neman shugabancin Amurka.