'Yammacin duniya na yin kafar-ungulu a yaki da ta'addanci'

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Putin ya ce kasashen yammacin duniya na maimaita irin kuskuren da suka yi a baya

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya zargi kasashen yammacin duniya da gazawa wajen hada gwiwa da kasarsa domin yaki da ta'addanci.

A wani jawabi da ya gabatar a majalisar wakilan kasar, Mr Putin ya ce kasashen yammacin duniya suna maimaita irin kuskuren da suka yi kafin yakin duniya na biyu, lokacin da wasu kasashe suka gaza bin kiran da tsohuwar tarayyar Soviet ta yi na hada kai domin tunkarar barazanar 'yan Nazi.

Mr Putin ya ce kungiyar tsaro ta NATO tana kara kaimi wajen kai hare-hare a kusa da kan iyakokin Rasha.

Ya kara da cewa hakan zai zamarwa kasarsa ta yi kyakkyawan shiri na yin raddi.