Mazauna kauyuka a Bauchi sun koka da matsalar 'yan bindiga

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army

A jihar Bauchin Nijeriya, al'umomin wasu yankunan musamman na kauyuka dake makotaka da wasu manyan dazuka na ci gaba da kokawa da matsalar 'yan bindiga dake kai hare-hare da satar mutane suna garkuwa da su, musamman a baya-bayan nan.

Al'umomin dai na zargin cewa hukumomi basa hobbasan a zo a gani wajen yaki da matsalar, amma hukumomin na cewa suna bakin kokarinsu, inda ma suke kama mutane da dama da ake zargi da aikata laifin satar mutanen domin neman kudin fansa.

Mazauna yankuna sun bayyana cewa, ga dukkan alamu wasu daga cikin 'yan bindigar barayin shanu ne da masu garkuwar da mutane d aka fatattake su daga dajin Falgore wanda ya ratsa jihohi da dama.

Sun ce sun kai kokensu ga mahukunta amma kuma har yanzu ba su samu wani dauki ba.

A nasu bangaren, mahukuntan sunce suna kokari wajen yakar irin wadannan bata gari inda sukan bisu har maboyarsu, sai dai kuma sukan fuskanci wasu kalubale a yayin samamen mutanen.