'Yan Biritaniya na yin zabe kan EU

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan kasar Biritaniya na kada kuri'unsu na raba-gardama a kan ko kasar ta zauna ko kuwa ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai ranar Alhamis.

Wata kididdiga ta nuna cewa mutum 46,499,537 suka cancanci kada kuri'insu a zaben.

An bude rumfunan zabe da misalin karfe 07:00 a agogon kasar, kuma za a kammala zaben da misalin karfe goma na dare.

Wannan shi ne karo na uku da 'yan Biritaniya ke kada kuri'ar raba-garma a tarihin kasar, kuma hakan na faruwa ne bayan an kwashe wata hudu ana zazzafar muhawara kan batun.

A al'adar watsa labarai, BBC za ta kawo bayanai ne kawai a lokacin da aka fara kada kuri'a, sai dai za ku iya ganin sakamakon zaben bayan an kammala shi.