Masu fina-finan batsa sun nemi afuwa a Japan

Kungiyar masu daukar nauyun yin fina-finan batsa a kasar Japan sun nemi afuwa bayan zargin da aka yi cewa suna tursasawa wasu mata suna yin fina-finan batsa.

Kungiyar ta ce "muna matukar neman gafara" bisa rashin daukar mataki kan wannan lamari a baya.

A farkon wannan watan ne aka kama uku daga cikin jami'an kungiyar bayan zargin da aka yi cewa sun yi wa wata mace barazana sanna suka tilast mata shiga fina-finan batsa fiye da 100.

Kazalika ana zargin wasu masu shirya fina-finan batsan da tsoratar da mata, musamman kanana yara domin su sanya hannu a kan kwantaragin yin fina-finan batsa.