Dokar yaki da kwayoyin sa kuzari a Kenya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An taba zargin wasu 'yan tseren kasar Kenya da afa kwayoyi masu kara kuzari

Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sanya hannu a kan kudurin dokar yaki da shan kwayoyi masu kara kuzari a wani yunkuri na bai wa 'yan wasan tseren kasar damar shiga gasar Olympics a Rio.

Ya sanya hannu kan sabuwar dokar ne wata guda bayan da hukumar yaki da shan kwayoyi masu kara kuzari ta duniya ta ce Kenya na cikin kasashen da ke karya dokokin hana coge a wasanni.

'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Kenya fiye da 40 ne aka dakatar saboda shan kwayoyi masu kara kuzari a cikin shekara biyun da suka gabata.

A farkon wannan makon, kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya ya ce dole ne sai 'yan wasan kasashen Kenya da Rasha sun haye gwajin da aka yi musu na amfani da kwayoyi masu kara kuzari idan har suna son su shiga gasar ta bana a birnin Rio.