Nigeria: Sabodin tsari a hukumar kula da sufurin jiragen ruwa

Hakkin mallakar hoto AFP

A Nigeria hukumar kula da sufurin jiragen ruwa wato Nigerian Shippers Council ta fitar da wani tsari da zai tabbatar da ana fitar da kaya daga tashoshin jiragen ruwa ta hanyoyin zamani da suka hada da amfani da shafin internet.

Sabon tsarin ya kuma hada da hanyar kawar da cin hanci da rashawa ta hanyar rage mu'amalar mutum-da-mutum a wajen fitar da kaya daga tashohin jiragen ruwa.

A baya dai tashohin jiragen ruwan Nigeria dai sun yi kaurin suna ta fuskar cin hanci da rashawa, da wasu ke ganin yana kawo tarnaki ga bunkasa kasuwanci a kasar.

Shugaban hukumar ta Nigerian Shippers Council, Malam Hassan Bello ya bayyana cewa,an fitar da wannan sabon tsari ne saboda ba a bin tsarin da ya kamata a hukumar, kowa na abin da yaga dama.

Ya kara da cewa za a kawo sabbin tsarin da ba sai kaje fitar da kayanka ba, injina ne kawai za su rika aiki wajen fitar da kaya, kuma yin hakan zai taimaka wajen rage cin hanci da rashawa a hukumar.