''Ana sace abincin 'yan gudun hijira ''

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Boko Haram ya raba mutane miliyan biyu da muhallansu

Majalisar wakilan Nigeria ta tafka mahawara game da wani korafi da aka gabatar mata na sacewa da kuma wawashe kayayyakin da ake kai wa 'yan gudun hjira ciki har da abinci.

Majalisar ta bayyana al'amarin a matsayin abin takaici bayan an yi doguwar muhawara.

Majalisar wakilan ta kuma amince da cewa ya zama wajibi ne hukumomin tsaro da suka hada da na 'yan sanda da 'yan sandan ciki da kuma hukumar EFCC su gudanar da bincike game da wannan al'amari da kuma hukunta duk wadanda aka samu da sace kayayyakin 'yan gudun hijirar.

Dan majalisar wakilan Nigeriar Honourable Magaji Da'u Aliyu ya shaidawa BBC cewa 'majalisar za ta kafa wani karamin kwamiti wanda zai tabbatar da an bi kadin abinda aka tattauna a majalisar a cikin kwana bakwai.'

Har ila yau kwamitin zai zaga zuwa sansanonin 'yan gudun hijirar domin ya ganewa idanunsa sannan kuma ya yi tambaya game da abinda ke faruwa