Rigakafin cutar shawara a Angola da Congo

Image caption Ciwon Shawara ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutum 350 a kasar Angola inda cutar ta fara

Hukumar lafiya ta duniya, WHO za ta fara yin rigakafin cutar shawara a kan iyakar da ke tsakanin kasar Angola da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a wani yunkuri na hana yaduwar cutar.

Riagakafin, wanda za a fara a makon gaba, zai kuma mayar da hankali kan mazauna Kinshasa, babban birnin Congo inda aka ayyana cutar a matsayin annoba.

Barkewar ciwon shawarar, wanda shi ne mafi muni a shekaru da dama, ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutum 350 a kasar Angola inda cutar ta fara, kuma mutum sama da 70 ne suka mutu a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

An yi amfani da tarin magungunan rigakafin ciwon shawara na duniya, musamman saboda girman cutar a kasar Angola.