Ko ficewar Birtaniya da ga tarayyar turai ta yiwa Commonwealth dadi?

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Birtaniya ta fice daga kungiyar tarayyar turai

Nigel Farage shi ne shugaban jam'iyyar Independence Party, kuma ya na daya daga cikin jagororin da suka rika fafutukar ganin Birtaniya ta fice daga kungiyar tarayyar turai.

Bayan da aka sanar da ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar tarayyar turai, Farage, ya furta cewa ficewar Birtaniyar zai ba ta damar karfafa huldar da ke tsakaninta da wasu kasashe.

Ya jadada cewa musaman huldarta da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka wadanda ke cikin kungiyar Commonwealth.

A nata ra'ayin Baroness Scotland, sakatariyar kungiyar Commonwealth da aka tambaye ta shin ko kasashen Commonwealth sun yi farin ciki da ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar tarrayar turai?

A kan wannan sai ta ce, " na farko shi ne al'ummar Birtaniya sun bayyana matsayin su, kuma mun sha yin magana a kan muhimmancin demokradiyya, wanda ya ke tsari ne da ke bada damar gabatar da shiri tare da bai wa jama'a damar amincewa da shi".