Niger: Mai rajin kare hakki zai sha dauri

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mahamadou Issoufou shugaban kasar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, wata kotu a Yamai ta wa wani dan rajin kara hakkin dan adam hukuncin da sai ya sake aikata laifi kafin a aiwatar da shi.

Kotun ta kuma ci Abdul Usman Mumuni tarar jaka 50 na kudin Sefa.

An same shi da laifin rubuta wasu kalaman batanci a shafin sada zumunta na Facebook kan shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou game da yakin da kasar ke yi da mayakan kungiyar Boko Haram.

Shi dai mai fafutikar ya nuna kasawar shugaban kasar game da yaki da kungiyar ta Boko Haram.

Kungiyar Amnesty International dai ta ce hukuncin wata hanya ce ta hana mutane fadar albarkacin bakinsu.