Basket Ball: Kano Pillars da Customs za su wakilci Najeriya

Kungiyar kwallon kwando ta Kano Pillars ta kai wasan karshe a gasar zakaru takwas ta Nigeria, bayan da ta ci Kwara Falcons da ci 71 da 56 a fafatawar da suka yi a jiya a jihar Legas.

Hakan na nufin Pillars din za ta buga wasan karshe a yau Asabar da Customs, wadda ta samu nasara a kan Royal Hoopers da ci 69 da 47 a dai ranar ta Juma'a.

Da wannan sakamakon Kano Pillars da Customs ne za su wakilci Nigeria, a gasar kwallon kwando ta zakarun nahiyar Afirka da za a yi a nan gaba.

Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada ya tambayi kociyan Kano Pillars, Alhaji Sani Ahmed kan nasarar da suka yi na kai wa wasan karshe kuma karo na biyu a jere, ga abinda yake cewa;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti