Senegal ta yi wa Karim Wade afuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ci shi tarar $230m a kan mallakar akalla $200m ba bisa ka'ida ba

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya sanya hannu a wata dokar yi wa dan tsohon shugaban kasar Abdullahi Wade, wato Karim Wade afuwa bisa tuhumar cin hanci da rashawa.

An dai yanke wa Karim Wade hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara shida a shekarar da ta gabata.

Sai dai Shugaba Sall ya wanke Karim Wade da wasu mutum biyu da aka tsare su tare, amma duk da haka sai sun biya kudin da aka tuhume su da sacewa.

An ci shi tarar $230m a kan mallakar akalla $200m ba bisa ka'ida ba.

Rahotannin na cewa tuni Karim Wade ya bar Senegal zuwa ko Faransa ko kuma Qatar.

A shekarar 2012 aka tuhume shi da laifin cin hanci bayan Shugaba Macky Sall ya lashe zaben shugaban kasar, wanda ya kayar da mahafinsa.