Zuma ya fuskanci koma-baya kan cin hanci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan shi ne koma baya ta fannin shari'a na baya-bayan nan da Jacob Zuma ke fuskanta

Wata kotu a kasar Afrika ta kudu ta hana shugaba Jacob Zuma da masu shigar da kara damar daukaka kara a kan shawarar da ta yanke cewa za a kama shi da laifin cin hanci a kan badakalar makamai da darajarsu ta kai biliyoyin daloli a shekarar 1999.

A shawarar da kuton ta yanke, ta kara da cewa "Babu wani amfanin" musun da ake na neman damar daukaka kara.

A watan Afrilu ne dai kotun ta yanke hukuncin cewa shawara da aka yanke a shekarar 2009 ta janye laifuka 783 da ake tuhumar Mista Zuma da aikata wa ba a yi ta kan ka'ida ba.

Sai dai Mista Jacob Zuma ya sha musanta zargin da ake yi na cewa ya karbi cin hanci a kan batun sayen makamai.