Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai

Hakkin mallakar hoto iStock

Al'ummar Birtaniya sun kada kuri'ar amincewa su fice daga kungiyar Tarayyar Turai.

Duk da cewa ba a bayyana sakamakon karshe ba, rahotanni da muka tattara daga sassa da dama sun nuna cewa masu neman kasar ta fice ne suka yi nasara.

Wannan sakamako zai kawo karshen sama da shekaru 40 da kasar ta shafe a kungiyar.

Tuni darajar kudin kasar, fan, ta yi faduwa mafi muni tun shekarar 1985.

Nan gaba kadan ne ake sa ran Fira Minista David Cameron, wanda ya nemi jama'a su goyi bayan ci gaba da zama a kungiyar, zai yi jawabi ga al'ummar kasar.

Ya na fuskantar matsin lamba kan yadda sakamakon zaben ya raba kawunan 'yan kasar.