EU ta nemi Biritaniya ta hanzarta ficewa

Hakkin mallakar hoto EPA

Kasashen da suka kafa kungiyar Tarayyar Turai sun sake bayyana bukatarsu na Biritaniya ta yi hanzarin ficewa daga kungiyar.

A wani taron gaggawar da suka yi ranar Asabar a Berlin, ministocin kasashen sun tattauna akan kuri'ar da 'yan Biritaniya suka kada ta ficewa daga kungiyar.

Ministan harkokin kasashen waje na Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya yi kira ga Biritaniya da ta yi sauri ta fita domin kungiyar ta fuskanci harkokin dake gabanta.

Ya ce duk da cewa Tarayyar Turan tana mutunta shawarar da Biritaniyar ta zartar na ficewa daga cikinta, hakkin Turan ne ta maida hankalinta wajen lura da harkokin kungiyar, malmakon bata lokacin kan Biritaniyar.

Kasashe shidda -- wadanda sune tushen kafa kungiyar kimanin shekaru 60 da suka gabata -- sune suka yi taron gaggawar a Berlin.

Kasashen kuwa sune Jamus da Faransa da Italiya da Belgium da Luxembourg da kuma Netherlands.

Biritaniya, wadda ta kada kuri'ar shiga kungiyar a shekarar 1975, ta kada kuri'ar ficewa daga cikinta bayan da Firaminista David Cameron ya amince da gudanar da kuri'ar raba gardama a ranar Alhamis.

Mista Cameron ya yi shelar sauka daga mukaminsa bayan ya gaza shawo kan 'yan Biritaniyar su amince da cigaba da kasancewa cikin kungiyar.

Ya ce zai sauka nan da zuwa watan Oktoba domin wanda zai gaje shi ya samu damar aiwatar da tattaunawa da kungiyar Tarayyar Turan akan ficewar Biritaniyan.

Karin bayani