An kammala kada kuri'a a zaben shugaban kasar Iceland.

Hakkin mallakar hoto AFP

An kammala kada kuri'a a zaben shugaban kasar Iceland.

Wanda ake ganin zai iya samun nasara a zaben shi ne Guðni Jóhannesson, masanin tarihi wanda ba shi da kwarewa a aikin gwamnati.

Sai dai nasarar da 'yan wasan kwallon kafa na kasar suka yi a gasar cin kofin nahiyar da akeyi a Faransa ya sa 'yan kasar ba su mayar da hankali a kan takarar kujerar shugaban kasar ba.

An dai amanna cewa kusan kashi goma cikin dari na al'ummar kasar sun bar kasar domin zuwa kallon wasan da yan kwallon kafarsu suka yi wanda shi ne karon farko.