Nigeria: Zanga-zanga a Ado Ekiti

Hakkin mallakar hoto ekiti state government
Image caption gwamnan ekiti

A Najeriya daruruwan mutane a garin Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti suka fara wata zanga-zanga ta sai baba ta gani.

Masu zanga-zangar na neman gwamnan jihar Ayodele Fayose da ya sauka daga kan mukaminsa.

An yi zanga-zangar saboda kasa biyan albashi da gwamnati tayi na tsawon wasu watanni, to amma gwamnatin jihar ta ce wannan bita da kulle ne na siyasa kawai aka shirya.

Haka zalika, ana tuhumar gwamnan jihar da karbar wasu makudan kudi daga cikin kudin da aka kebe domin sayan makamai a lokacin mulkin shugaba Goodluck Jonathan.

Gwamnan dai ya musanta hakan a lokacin da jama'a ke son ya fito ya yi bayani.