Somalia: Al Shabaab sun kai hari a wani otel

Hakkin mallakar hoto AFP

An samu fashewar wani abu mai karar gaske a wani otel da ke Mogadishu babban kasar Somalia.

Wani jami'i a kasar Somaliya ya ce mayakan kungiyar Al Shabaab sun kutsa kai cikin otel din Naso Hablood kuma ana can ana gwabza kazamin fada.

Rahotanni sun ce sun yi amfani da wata mota da ke makare da bama bamai wadda ta tashi domin shiga cikin otel din.

Mayakan kungiyar ta Al Shabaab kan kai hare hare a otel otel din da ke Mogadishu musaman wadanda jami'an gwamnatin suke sauka a ciki.

Lamarin kan kuma shafi fararen hular da ba su ji basu gani ba.