Ana zabe a Spaniya

Hakkin mallakar hoto Getty

Masu kada kuri'a a Spaniya sun fara tafiya rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a wani yunkuri na kawo karshe rikicin siyasar da ya biyo bayan babban zaben kasar watanni shida da suka gabata.

Manyan jam'iyyun adawar kasar biyu masu ra'ayi daban-daban sun kunno kai, inda suka karya lagon Babbar jam'iyyar kasar ta Conservative mai tsattsauran ra'ayi.

Duk kokarin da akayi na kafa gwamnatin hadin kai ya ci tura lamarin da ya janyo sake gudanar da zaben.

Ana dai yi hasashen cewa za a kafa majalisar dokokin da babu jam'iyya mai rinjaye a cikinta a kasar.